Isa ga babban shafi

Dan sandan Tunisiya ya kashe masu ibadar Yahudawa da jami'an tsaro

Akalla masu Ibadan shekara shekara na yahudawa biyu da ‘yan sanda biyu aka kashe a wata shahararriyar mujami'ar kasar Tunisiya a ranar Talata a wani hari da wani dan sanda ya kai.

Mujami'ar ibadan shekara-shekara ta Yahudawa a Ghriba dake  Djerba na kasar Tunisiya 15/05/2006
Mujami'ar ibadan shekara-shekara ta Yahudawa a Ghriba dake Djerba na kasar Tunisiya 15/05/2006 AP - HASSENE DRIDI
Talla

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisiya ta ce wasu mutane hudu da suka ziyarci mujami'ar Ghriba da ke tsibirin Djerba tare da wasu jami'an tsaro biyar sun jikkata a harin kafin a kashe maharin.

Mujami'ar ibadan shekara-shekara ta Yahudawa a Ghriba dake  Djerba na kasar Tunisiya 9/05/2002
Mujami'ar ibadan shekara-shekara ta Yahudawa a Ghriba dake Djerba na kasar Tunisiya 9/05/2002 AP - HASSENE DRIDI

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Tunisiya ta fitar ta bayyana masu Ibadan biyu da aka kashe amatsayin daya dan kasar Tunusiya ne mai shekaru 30 da kuma Ba-Faranshe mai shekaru 42, sai dai ba a bayyana sunayensu ba.

An kai harin ne bayan da maharin ya fara harbin wani abokin aikinsa tare da daukar harsashi kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.