Isa ga babban shafi

Wani dan Tunisia ya jikkata 'yan sandan dake gadin wurin bautar Yahudawa

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisia ta ce wani mahari dauke da wuka ya raunata wasu 'yan sanda biyu dake gadin wani wurin bautar yahudawa dake tsakiyar Tunis, babban birnin kasar.

'Yan sandan kasar Tunisia
'Yan sandan kasar Tunisia © REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan Fakher Bouzghaya ya shaida wa kamfanin dillancin Labarai na AFP cewa a baya an taba daure mutumin bisa laifin "ta'addanci" aka kuma sake shi a shekarar 2021.

Bouzghaya ya kara da cewar ana gudanar da bincike kan harin.

Kafin samun 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1956, Tunisia ta kasance gida ga Yahudawa sama da 100,000, amma kaurar da suke yi ya sanya a yanzu adadinsu bai wuce kimanin dubu guda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.