Isa ga babban shafi

Burkina Faso: Adadin mutanen da aka kashe a Karma ya kai 136

Wata kungiyar kare hakkin dan adam a Burkina Faso ta ce adadin fararen hula da aka kashe a kauyen Karma da ke yankin arewacin Burkina Faso a ranar 20 ga watan afrilun nan, ya kai 136, cikinsu akwai mata 50 da kananan yara 21.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso The Washington Post via Getty Im - The Washington Post
Talla

Kididdigar da kungiyar ta fitar a ranar juma’a da ta gabata game da kisan ya kuma nuna jarirai 30, ‘yan kasa da wata 1 na daga cikin wadanda mayakan suka kashe.

Wasu ‘yan bindiga sanye da kayan soji ne suka farwa kauyen, inda  suka yi wa mutane da dama kisan gilla, harin da ke zuwa bayan wanda wasu mayaka masu ikirarin jihadi suka kai wani wuri kusan da kauyen Karma a ranar 15 ga watan Afrilun nan inda suka kashe sojoji 6 da wsu 34.

Kungiyar ta kuma ce baya ga wadannan, maharan sun kuma farwa wasu kauyuka na daban, inda suka kashe mutane 6 a kauyen Dinguiri, wasu 2 a Ménè, sannan suka kashe wasu mutanen 3 a kan hanyar dake tsakanin kauyukan Ouahigouya da Barga.

Adadin mamatan da alkalin Ouahigouya dake yankin arewacin kasar ya sanar a ranar lahadi na nuna kusan mutane 60 aka kashe a mabanbantan hare haren, saidai mazauna kauyen Karma da wasu shaidun gani da ido sun ce adadin ya zarce 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.