Isa ga babban shafi

Mutane 140 ne suka mutu sakamakon rikicin ta’addanci a Togo

Akalla sojoji 40 da fararen hula 100 ne aka kashe a yankin arewacin Togo sakamakon rikicin masu ikirarin jihadi da ya daidaita yankin, a cewar shugaban Kasar Faure Gnassingbe yayin zantawarsa da manema labarai karon farko tun bayan da ya gaji mulki daga mahaifinsa a shekarar 2005.

Shugaban Kasar Togo, Faure Gnassingbé
Shugaban Kasar Togo, Faure Gnassingbé © LUDOVIC MARIN/AFP
Talla

Shugaban ya dora alhakin lamarin da kasarsa ta shiga a kan kungoyin IS da wata kungiya ta daban da ke da alaka da al-Qaeda.

Yayin zantawarsa da gidan talabijin na Kasar a ranar alhamis, Gnassingbe ya ce Kasar ta tafka asara musamman ta bangaren jami’an tsaro, inda aka kashe akalla sojoji 40 da fararen hula 100.

 

Shugaban mai shekaru 56 a duniya, wanda a karo na 3 kenan yake komawa kan karagar mulkin Togo, ya bayyana damuwa a kan yadda gwamnati da bangaren tsaro suka yi gum game da hare haren da mayakan ke kai wa babu kakkautawa.

Kasar Togo dake yankin yammacin Afrika da kasashen Benin da Ghana da kuma Ivory Coast dake makotaka da ita, na cigaba da fama da barazanar rikice rikicen ta’addanci da suka samo asali daga Burkina faso da Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.