Isa ga babban shafi

An fara tattaunawar sulhu tsakanin Habasha da 'yan tawayen Oromo

An fara tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Habasha da ‘yan tawayen yankin Oromiya na kungiyar OLA a Zanzibar, yanki mai kwaryakwaryar cin gashin kansa da ke kasar Tanzania.

Sojojin Habasha yayin kokarin tabbatar da doka da oda a garin Bisoftu na yankin Oromia, bayan kafa dokar ta baci a shekkarar 2016.
Sojojin Habasha yayin kokarin tabbatar da doka da oda a garin Bisoftu na yankin Oromia, bayan kafa dokar ta baci a shekkarar 2016. AP - STR
Talla

‘Yan tawayen na Oromiya, daya daga cikin manyan yankuna 11 da suka yi wa birnin Addis Ababa kawanya, sun shafe gwamman shekaru suna yakar gwamnatin Habasha da zummar ballewa daga kasar.

Kungiyar OLA ta samo asali ne daga jam’iyyar adawar ‘yan kabilar Oromo da gwamnatin Habasha ta haramta bayan da yi kaurin suna wajen caccakar ta, a kan mayar da al’ummar yankin na Oromia saniyar ware.

Mayakan na OLA da gwamnatin Habasha sun dade suna zargin juna da hannu wajen kai wasu hare-hare da suka yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a yankin Oromia.

A cikin watan Fabarairun da ya gabata, hukumar kare hakkin dan adam ta Habasha ta dora alhakin harin da ya kashe fararen hula akalla 50 kan mayakan na OLA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.