Isa ga babban shafi

Gwamnatin Habasha za ta fara tattaunawa da 'yan tawayen Oromo

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya ce gwamnatinsa za ta fara tattaunawa da ‘yan tawayen yankin Oromia na kungiyar OLA, kuma ganawar sulhun za ta gudana ne cikin makon nan da muka shiga a kasar Tanzania.

Firaministan kasar Habsha Abiy Ahmad
Firaministan kasar Habsha Abiy Ahmad AP - Mulugeta Ayene
Talla

Wannan ne dai shi ne karo na farko da gwamnatin Habasha ta bayyana shirin ganawa da ‘yan tawayen na OLA, wadanda suka shafe gwamman shekaru suna fafatawa da sojojin gwamnati.

A cikin watana Fabarairun da ya gabata, hukumar kare hakkin dan adam ta Habasha ta dora alhakin harin da ya kashe fararen hula akalla 50 akan ‘yan tawayen na Oromo.

Kungiyar ‘yan tawayen dai ta samo asali ne daga jam’iyyar adawar ‘yan kabilar Oromo da gwamnatin Habasha ta haramta bayan da ta tsaurara wajen caccakar ta kan mayar da al’ummar yankin na Oromia saniyar ware.

Mayakan na OLA da gwamnatin Habasha sun dade suna zargin juna da hannu wajen kai wasu hare-hare a yankin Oromia inda aka kashe fararen hula da dama.

Fadan da ake gwabzawa tsakanin kungiyar OLA da gwamnatin Habasha dai bashi da alaka da fadan da ake yi a yankin Tigray, amma daga bisani sai mayakan na OLA suka kulla kawance da kungiyar ‘yan tawayen TPLF a yankin na Tigray.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.