Isa ga babban shafi
Habasha

An kashe 'yan kabilar Oromo sama da 140 a cewar HRW

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce akalla mutane 140 ne dukkaninsu ‘yan kabilar Oromo jam’ian tsaro suka kashe a kasar Habasha lokacin murkushe wata zanga-zangar da ‘yan kabilar ke yi don nuna adawa da shirin fadada birnin Adis-Abeba.

'Yan kabilar Oroma a Habasha
'Yan kabilar Oroma a Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

A karkashin wannan shiri dai gwamnati za ta kwace filayen noma wadanda mafi yawansu na ‘yan kabilar ta Oromo ne, to sai dai a cewar kungiyar ta Human Rights Watch, gwamnati ta bai wa jami’an tsaro damar yin amfani da karfi domin murkushe su tare da kashe akalla mutane 140 da kuma raunata wasu daruruwa.

Har ila yau kungiyar ta zargi hukumomin kasar da kama masu adawa da ita a siyasance, inda aka kama daya daga cikin jagoran ‘yan adawar amma har yanzu ba a san inda ake tsare da shi ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.