Isa ga babban shafi

Hatsarin jirgin ruwa ya lakume rayukan 'yan ci rani 34 a Libya

Jami’an agajin gaggawa a Libya sun tsamo gawarwakin wasu ‘yan ci rani 34, wadanda kwale-kwalensu na roba ya nutse a teku, kwanaki biyar da suka gabata.

Wasu 'yan ci rani da aka ceto daga nutsewa a tekun Meditaraniya.
Wasu 'yan ci rani da aka ceto daga nutsewa a tekun Meditaraniya. REUTERS - ANTONIO PARRINELLO
Talla

Bayanai sun ce kwale-kwalen robar na dauke ne da ‘yan ci rani kimanin 100 a lokacin da ya nutse a gabar tekun kasar ta Libya.

Rikicin da aka shafe fiye da shekaru goma ana yi a Libya, bayan kashe shugaba Mo’ammar Gaddhafi a shekarar 2011, ya mayar da kasar cibiyar kungiyoyi masu safarar mutane, wadanda ake zargi da cin zarafin ‘yan ci rani bayan karbe musu kudade, wani lokacin ma har da bautar da wasunsu.

A Tunisia da ke makwaftaka da Libya ma dai matsalar ‘yan ci ranin da ke neman tsallaka wa zuwa Tura ice ke karuwa.

A ranar Litinin da ta gabata, mahukuntan kasar suka bayyana cewa wasu bakin haure biyar daga yankin kudu da sahara sun nutse a cikin ruwa, yayin da kuma  aka gano gawarwakin wasu bakin hauren 31 da suka fara rubewa, bayan da euwan teku ya turo su waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.