Isa ga babban shafi

Dubban bakin haure ne ke makalewa a Arewacin Nijar - IOM

Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta ce ta damu matuka game da karuwar bakin haure da ke rayuwa cikin mawuyacin hali a Assamaka da ke yankin Agadez a arewacin Jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin bakin haure da ke neman zuwa Turai ta tekun Libya
Wasu daga cikin bakin haure da ke neman zuwa Turai ta tekun Libya Taha JAWASHI / AFP
Talla

Kimanin bakin haure 7,700 ne ke makale a Nijar a halin yanzu kuma suna cikin tsananin bukatar abinci, ruwan sha mai tsafta, matsuguni, magunguna da kariya, in ji sanarwar da hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta fitar.

Akalla mutane 5,000 ne suka makale a garin Assamaka, kauye na farko da ke kan iyakar Nijar da Aljeriya.

Yawancin bakin hauren dai sun fito ne daga kudu da hamadar Sahara ne, amma ana samun ‘yan kasashen Siriya da ma 'yan Bangladesh a cikin su, kuma bayanai sun ce daga kan iyakar, bakin haure na bukatar tafiyar akalla kilomita 15 ta cikin hamada domin isa gari ko cibiyar bayar da taimako.

Kamar yadda rahotanni ke cewa, kusan kowanne mako, kasar ta Aljeriya na tura daruruwan bakin haure kan iyakar.

A cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, adadin bakin hauren da ke makale a arewacin Nijar a halin yanzu ya karu da kashi 35% a shekarar 2022.

A cikin wannan shekarar, IOM ta ce ta taimaka wa bakin haure fiye da 17,000 a yankin, adadin da ta ce na ci gaba da karuwa a shekarar 2023.

Da dama daga cikin bakin hauren da ke makale a kan iyakar dai, an dawo da su ne daga kasashen Arewacin Afirka, irin su Aljeriya da kuma Libya.

Hukumar ta IOM ta ce tuni ta samar da cibiyoyi bakwai da ke kula da bakin hauren a yankunan Agadez da Yamai domin ba da taimako.

Galibin wadanda hukumar ta IOM ke taimakawa sun fito ne daga kasashen Mali da Guinea da Najeriya da kuma Saliyo.

Hukumar ta ce tana da kayan aiki ne kawai don taimaka wa bakin haure 1,500, amma a halin yanzu wasu bakin haure 3,500 ne ke jiran taimako a wajen cibiyar da ke bayar da taimakon gaggawa, musamman ga mutanen da ke cikin wani hali maras kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.