Isa ga babban shafi

Mauritania ta hallaka mayakan jihadi uku da suka tsere daga gidan yari

Gwamnatin Mauritania a yau asabar ta sanar da kashe mayakan jihadi uku da suka tsere daga gidan yari a ranar lahadin makon da ya gabata. An kama na hudu a arewacin kasar, yayin wani samame da aka kai inda aka kuma kashe wani Jandarma.

Sojojin kasar Chadi yayin atsaye a yankin Atar, dake Mauritania.
Sojojin kasar Chadi yayin atsaye a yankin Atar, dake Mauritania. US. Army/Sgt. Steven Lewis
Talla

Rahotanni daga hukumar tsaron Mauritania na cewa an kai harin ne cikin dare daga ranar juma'a zuwa asabar a yankin hamadar Adrar.

Mayakan jihadi guda hudu, da suka hada da dan kasar Mauritania Saleck Ould Cheikh Mohamedou, da ake kyautata zaton suna da matukar hadari kuma an yanke musu hukuncin kisa, sun tsere daga gidan yari a Nouakchott babban birnin kasar a ranar 5 ga watan maris na wannan shekara.

Wani yankin kasar Mauritania
Wani yankin kasar Mauritania © Xavier TESTELIN/Gamma-Rapho via Getty

Saleck Ould Cheikh Mohamedou na cikin wadanda aka kashe, in wani jami'in tsaron da ya nemi a sakaya sunansa.Gwamnati ba ta bayar da wannan karin haske ba a cikin sanarwar da ta fitar.

An kashe masu gadi biyu yayin tserewar ranar 5 ga maris.

Gudun wadanan yan kaso ya bata sunan Mauritania da ke yakar masu tsatsauran ra'ayin Islama. Saleck Ould Cheikh Mohamedou ya riga ya tsere daga gidan yari a shekarar 2015.

An nemi mutanen hudu da suka tsere tun daga lokacin. Bisa wasu bayanan sirri da ba a bayyana ba, sun kasance a wani yanki mai cike da tsaunuka a yankin Adrar, in ji ma'aikatar tsaro da harakokin cikin gida a cikin wata sanarwar hadin gwiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.