Isa ga babban shafi

Ghana na bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kai daga Birtaniya

Yau Ghana ke cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai daga Birtaniya, bikin zagayowar ranar ‘yancin da a wannan karon ke zuwa a wani yanayi da kasar ke fama da mummunan koma bayan tattalin arziki.

Wani faretin Sojin Ghana don girmama zagayowar ranar ta samun 'yanci.
Wani faretin Sojin Ghana don girmama zagayowar ranar ta samun 'yanci. © AF
Talla

Fiye da ‘yan Ghana dubu 5 suka halarci bikin ranar ta yau daga sassa daban-daban na kasar kama daga manyan malaman addinai da sarakunan gargajiya.

Kamar yadda shugaba Nana Akufo-Addo ya shaida a shekarar 2017 kan yadda za a rika raba wuraren da za a rika gudanar da bikin tunawa da ranar ‘yancin daga yanki-zuwa yanki maimakon tsayawa a waje guda

A wannan karon an gudanar da gangamin zagayowar ranar ce a cibiyar matasa da ke yankin Adaklu a Volta, ranar da a wannan karon aka yi mata take da ‘‘Hadin kanmu, karfinmu kuma manufarmu’’.

Tun da safiyar yau ne shugaba Nana Akufo-Addo ya gabatar da jawabi ga al’ummar kasa dangane da ranar ta yau wadda aka gudanar da faretin ban girma da sojojin kasar da sauran bangarorin jami’an tsaro.

A ranar 6 ga watan Maris din 1957 ne Ghana ta samu ‘yanci daga bayan shafe shekaru 83 karkashin mulkin mallakar turawan Birtaniya.

Shugaban Ghana na farko Dr Kwame Nkrumah ne ya sanar da ‘yancin kasar wadda cikin bayaninsa ya bayyana cewa daga ranar ta 6 ga watan Maris 1957 ba sa karkashin mulkin mallakar Turawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.