Isa ga babban shafi

An shiga fargaba a Ghana bayan wani yunkuri na karya gada da Bam

Kame wasu batagari da ke kokarin karya wata babbar gada a Ghana ta hanyar amfani da ababen fashewa irinsa na farko a tarihin kasar ya sake sanya fargaba a zukatan jama’a kan yiwuwar shigowar ayyukan ta’addanci daga makwabciyar kasar Burkina Faso. 

'Yan sandan Ghana
'Yan sandan Ghana alternativeafrica
Talla

Ghana da takwarorinta kasashen yankin tekun Guinea da suka kunshi Benin da Ivory Coast da kuma Togo na cike da fargabar fantsuwar ayyukan ta’addanci daga makwabtansu kasashen Sahel da ke fama da matsalolin kungiyoyin mayakan ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi.

Tuni dai kasashen Benin da Ivory Coast da kuma Togo suka fuskanci hare-hare da kuma kutse a kan iyakokinsu, amma kawo yanzu Ghana ta tsallake rijiya da baya daga harin kai tsaye da ake dangantawa da masu kaifin kishin Islama a Burkina Faso.

Ministan tsaron Ghana Dominic Nitiwul ya shaidawa majalisar dokokin kasar a wannan makon cewa masu aikata laifuka sun yi yunkurin tarwatsa wata gada ta hanyar amfani da wasu bama-bamai a yankin Bawku da ke kusa da kan iyaka a ranar Litinin da ta gabata.

Rikicin kabilanci

Bawku dai ya fada cikin rikici na tsawon shekaru da dama tsakanin al'umomin biyu masu gaba da juna wanda wasu masana ke fargabar zai iya haifar da rashin zaman lafiya tare da baiwa mayakan masu ikirarin jihadi damar kutsawa cikin Ghana.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.