An kawo karshen bikin nuna fina-finan Africa na shekara shekara a Burkina Faso
A bikin fina-finan Afirka na Fespaco na shekara-shekara dake gudana kasar Burkina Faso ,dan kasar Tunisia Youssef Chebbi ne ya lashe kyautar Stallion of Yennenga a jiya asabar.
Wallafawa ranar:
Youssef Chebbi, haifaffen Tunisia, wanda fim dinsa ya shafi binciken kisan gillar da aka yi wa wani ma'aikacin gini a Carthage da ke wajen birnin na Tunis , bai halarci bikin da aka yi a Burkina Faso ba, wanda shugaban mulkin soji Ibrahim Traore ya jagoranta.
Chebbi ya samu nasara akan abokin hamayyar Burkina Faso Apolline Traore, wanda ya samu lambar yabo ta Silver Stallion na "Sira", yayin da tagulla ta tafi ga Angela Wamai ta Kenya.
Fina-finai kusan 170 a sassa daban-daban aka baiwa jama'a damar bayyana ra'ayyin su a kai da taken "Cinema na Afirka da al'adun zaman lafiya".
Kasar Tunisiya ta yi nasara a wannan bikin na fina-finan Afirka, a daidai lokacin da daruruwan 'yan kasar daga yankin kudu da hamadar Sahara ke tserewa daga kasar saboda hare-hare da zanga-zangar nuna kyama biyo bayan kalaman shugaban kasar Kais Saïed ya yi kan 'yan ciranin ba bisa ka'ida ba.
An ba da kyautar wasan kwaikwayo mafi kyau ga "Bleu du Caftan", 'yar Morocco Maryam Touzani.
An gudanar da wannan buki karo na 28 cikin wani yanayi mai tsananin tsaro a Burkina, wanda tashe tashen hankulan masu da'awar jihadi suka girgiza tsawon shekaru da dama.
Za a sake gudanar da irin wannan biki na Fespaco daga 22 ga Fabrairu zuwa Maris 1, 2025 a Burkina Faso..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu