Isa ga babban shafi

An cika shekaru 12 da hambarar da gwamnatin Moammar Gaddafi na Libya

An cika shekaru 12 da hambarar da gwamnatin Libya karkashin jagorancin marigayi Moammar Gaddafi inda dubban ‘yan kasar suka gudanar da gangamin murnar zagayowar ranar.

Tsohon shugaban kasar Libya Kanal Moammar Kadhafi.
Tsohon shugaban kasar Libya Kanal Moammar Kadhafi. (Photo : Reuters)
Talla

Dubban ‘yan Libya sun yi dandazo a biranen kasar musamman birnin Tripoli inda mutane suka yi dafifi  rike da tutocin kasar wadanda aka yiwa kwalliyar alfarma tare da rera waken hadin kan kasar da fatan kare rabe-raben kawuna.

Yayin gangamin na cika shekaru 12 da hambarar da gwamnatin ta Gadhafi da ya gudana ranar juma’ar da ta gabata, dakarun Sojin Libya sun kuma gudanar da faretin ban girma don girmama kawar da waccan gwamnati da ta shafe gomman shekaru ta na mulkar kasar ta arewacin Afrika.   

Gangamin cika shekaru 12 da kawar da gwamnatin Gadhafi a Libya.
Gangamin cika shekaru 12 da kawar da gwamnatin Gadhafi a Libya. REUTERS/Ismail Zitouny

Gangamin tunawa da juyin-juya halin na shekarar 2011 ya zo ne duk da rikicin siyasar da kasar ke gani na gaza zabar shugaba guda da zai mulki kasar.

Sai dai Rabie Imran guda cikin masu gangamin, ya ce suna fatan shekara mai zuwa a iya gudanar da zabe a kasar wanda zai kawo karshen rarrabuwar kai tare da samun shugaba guda da zai jagorance su.

An dai gaza gudanar da zabe a kasar ta Libya duk da shirye-shiryen da aka yi don aiwatar da shi a watan Disamban 2021 inda yanzu haka ake da shugabanci biyu a kasar.

A ranar 17 ga watan Fabarairun 2011 ne juyin-juya halin da kasashen larabawa suka fuskanta ya yi awon gaba da jagoranci Kanal Moammar Gadhafi da ya shafe shekaru 42 yana mulkin kasar ta Libya biyo bayan hadakar sa Sojojin kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Amurka bvaya ga taimakon NATO suka yiwa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.