Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta fara bincike kan zargin kisan 'yan Najeriya da Sojinta suka yi

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta kaddamar da bincike kan zargin kisan wasu ‘yan Najeriya da suka ratsa kasar akan hanyarsu ta isa Senegal don ziyarar ibada a Kaulaha.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso © AFP
Talla

Ministan harkokin wajen Burkina Faso Olivia Rouamba da ke bayani kan bude binciken ya ce gwamnatin kasar za ta gudanar da bincike tare da tabbatar da adalci akan zargin kisan ‘yan Najeriya.

Bayanai sun ce ‘yan Najeriyar mabiya darikar Tijjaniyya makare a wata motar Safa sun ratsa kasar ta Burkina Faso ne don isa Kaulawa amma kuma Sojojin Burkina Fason suka bude musu wuta.

Wasu jaridun Najeriya sun ruwaito yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan mutanen yayin ganawarsa da Jakadan kasar a Burkina Faso Mistura Abdelraheem.

A cewar Mistura Abdelraheem tuni Burkina Fason ta fara bincike kan kisan fararen hular wadanda ba a bayyana adadinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.