Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan Najeriya mabiya darika

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar za a hukunta sojojin Burkina Faso da suka yi wa ‘yan Najeriya 16 mabiya Darikar Tijjaniyya kisan-gilla lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaulaha domin ziyarar ibada. 

Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan Najeriyar ba gaira babu dalili.
Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan Najeriyar ba gaira babu dalili. © AFP
Talla

Buhari ya ce suna tattaunawa da hukumomin sojin kasar domin ganin an hukunta wadannan jami’ai da suka wuce gona-da-iri wajen hallaka fararen hula. 

Rahotanni sun ce, wadannan mutane 16 daga kungiyar Jama’atu Ansaruddeen Attajinaya na kan hanyar zuwa mahaifar shugabansu, Sheikhul-Islam Ibrahim Niasse da ke Senegal lokacin da sojojin Burkina Faso da ke sintiri suka tare su a hanya, kana suka harbe su har lahira. 

Sakataren kungiyarsu Sayyidi Yahya ya ce sai da sojojin suka zabi wasu daga cikin tawagar matafiyan, kafin su bude wuta akan wadannan 16 ba tare da wani dalili ba. 

Shugaban Najeriya wanda ya bayyana kaduwarsa da kisan-gillar ta sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya raba wa manema labarai, ya ce Ma’aikatar Harkokin Najeriya ta dauki maganar inda take tattaunawa da hukumomin Burkina Faso domin gudanar da bincike da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. 

Buhari ya kuma jaddada cewar gwamnatin Najeriya za ta yi iya bakin kokarinta domin kwaso gawarwakinsu da kuma sauran matafiyan da suka samu raunuka domin dawo da su gida. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.