Isa ga babban shafi

Firaministar Italiya Giorgia Meloni a Libya don sanya hannu kan yarjejeniyar gas

Italiya, kamar sauran kasashen Turai masu son maye gurbin iskar gas da suke shigo shi daga Rasha, za ta rattaba hannu kan kwangilar hako iskar gas daga Libya. Sanarwa daga Farhat Ghadara, shugaban kamfanin samar da iskar gas na kasar Libya (NOC). 

Giorgia Meloni Firaministar kasar Italiya
Giorgia Meloni Firaministar kasar Italiya REUTERS - GUGLIELMO MANGIAPANE
Talla

Yarjejeniya da za ta cimma tsakanin kasashen biyu Italiya da Libya a yau asabar a birnin Tripoli, a gaban Meloni, tare da babban kamfanin mai na Italiya ENI. Kwangilar ita ce mafi girma a bangaren samar da makamashin tsakanin kasashen na tsawon shekaru 25.

Shugabar gwamnatin Italiya ta na tafe ne tare da rakiyar  ministar harkokin wajenta da ministar harkokin cikin gida. 

A karkashin yarjejeniyar, kamfanin na ENI zai iya zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 8 a filayen iskar gas guda biyu a tekun Bahar Rum na kasar ta Libya. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.