Isa ga babban shafi

Bakin-hauren Libya na bukatar agajin gaggawa-MSF

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa, ta yi kira ga kasashen Turai da Arewacin Amurka, da sauran masu ruwa da staki, da su ba da kariya ga bakin haure da ke makale a Libya yanzu haka.

Migrantes esperan para cruzar la frontera entre Bolivia y Chile, en Colchane, Chile, el 1 de febrero de 2022.
Migrantes esperan para cruzar la frontera entre Bolivia y Chile, en Colchane, Chile, el 1 de febrero de 2022. REUTERS - STRINGER
Talla

MSF ta ce akwai bukatar a gaggauta kai dauki ga mutanen da suke cikin halin ni ‘ya su ta hanyar inganta shirin bude musu hanyoyin barin kasar.

Tun lokacin da aka fara ba da agajin jin kai ga bakin haure a Libya a shekarar 2016, MSF ke fuskantar rashin yiwuwar tabbatar da ci gaba da kula da lafiyar mutanen da ke fama da rashin lafiya, gami da wadanda aka azabtar da su, a ciki da wajen cibiyoyin da ake tsare mutane a kasar.

Shugabar sashen gudanarwa ga MSF a kasar ta Libya, Claudia Lodesani, ta ce "A Libya, ana tsare yawancin bakin haure ba bisa ka'ida ba, azabtarwa da kuma tashin hankali, ciki har da cin zarafin mata, sakamakon haka, hanyar da suke ganin ta dace su nemarwa kan su mafita ita ce kaura kuma hanyar Tekun Bahar Rum ita ce kadai tilo da za su bi.

’Yan tsirarun hanyoyin da doka ta basu damar zuwa kasashe da za su samu kwanciyar hankali, wanda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) da Hukumar Kula da kaura ta Duniya (IOM) suka kafa ba su da ingancin da za su karfafawa masu neman mafaka gwiwa.

A cewar rahoton, kasashe tara ne kawai za a yi la'akari da su wajen yin rijistar bakin cikin shirin sake tsugunar da su da UNHCR ta samar, kuma samun damar yin rajista kusan babu ga mutanen da ke wajen Tripoli, musamman wadanda suke makale a wuraren da ake tsare da su. A lokaci guda kuma, adadin da aka ware a kasashen da ya kamata su karbe an kayyade.

Rahoton ya gabatar da hanyoyin samar da mafita, kamar wadanda kungiyoyin agaji ke gudanarwa da hadin gwiwar gwamnatoci.

A Italiya, tuni aka samar da shirin jin kai, abin da ya bayar da damar kwashe wasu mutane masu rauni da ke bukatar kariya, ciki har da marasa lafiya da MSF ta basu kulawa a kasar Libya.

MSF na daya daga cikin kungiyoyin sa-kai na kasa da kasa da ke aiki a Libiya. Tawagar kungiyar na ba da tallafi na kiwon lafiya da sha’anin zamantakewa ga bakin haure da ke tsare a wuraren da aka tsare a wasu cibiyoyi har ma da wadanda ke tsare a gidaje na wucin gadi. MSF ta kuma shirya jigilar marasa lafiya zuwa asibiti tare da tallafa wa mutane don yin rajista karkashin shirin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD da kuma hukumar kaura ta duniya domin taimaka musu wajen ficewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.