Isa ga babban shafi

Libya ta kare yarjejeniyar hakar makamashin da ta kulla da Turkiya

Firaministan Libya Abdulhamid Dbeibah da ke birnin Tripoli, ya kare yarjejeniyar da ya kulla da Turkiya a farkon makon nan kan aikin hako mai da iskar gas a tekun Bahar Rum, lamarin da ya harzuka kasashen Turai.

Firaministan Libya Abdel Hamid Dbeibah.
Firaministan Libya Abdel Hamid Dbeibah. AP - Hazem Ahmed
Talla

Yarjejeniyar dai ta janyo suka daga Girka, da kuma masu adawa da Firaminista Dbeibah a Libya, inda a yanzu haka gwamnatoci biyu masu adawa da juna ke fafutukar mamaye madafun mulkin kasar.

A shekarar bara ne dai aka kafa gwamnatin Firaminista Dbeibah a Tripoli da ke yammacin kasar Libya a wani bangare na shirin samar da zaman lafiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai tun a watan Maris ‘yan adawa suka kafa wata gwamnatin a gabashin kasar, wadda ke kalubalantarsa, inda suka ce wa'adin Firaminista mai ci ya kare, kuma ba shi da hurumin sanya hannu kan yarjejeniyoyin kasa da kasa.

Karkashin sabuwar yarjejeniyar dai Turkiya za ta taimakawa Libya wajen aikin hakar makamashi a sassan kasar da kuma bayar da cikakken tsaro sashen hakar makamashin a kokarin farfado da koma bayan da sashen ya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.