Isa ga babban shafi

Sabon rikici a barke a yankin Amhara na Habasha

Rahotanni daga Habasha sun bayyana barkewar wani sabon rikicin kabilanci tsakanin kungiyoyin ‘yan kabilar Oromo da Amhara da ke tsakiyar kasar inda mutane da dama suka mutu daga dukkanin bangarorin biyu.

Yankin Amhara na Habasha.
Yankin Amhara na Habasha. AFP/Archivos
Talla

A cewar wasu ganau tun a karshen makon jiya ne rikicin ya faro can a kauyen Jewuha da ke yankin na Amhara wanda ya kai ga rasa asarar tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba, baya ga su kansu mayakan.

Kafofin labaran Habasha sun ruwaito cewa mayakan wadanda ke da alaka ta kurkusa da mayakan ‘yan tawaye masu fafutukar ‘yancin ‘yan kabilar Oromo sun farmaki wani sansani da ke karkashin kulawar mayakan Amhara tare da kashe jami’ai 20 hade da fararen hula 3.

A cewar kafofin rikicin ya fantsama zuwa wasu kauyuka tun daga litinin din makon nan ko da ya ke har yanzu gwamnatin kasar ba ta ce komi game da halin da ake ciki ba, yayinda rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin.

Rikicin dai na zuwa ne makwanni kalilan bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sojin Habashan da 'yan tawayen Tigray wadanda suka shafe kusan shekaru 2 suna gwabza yakin da ya ja hankalin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.