Isa ga babban shafi

Jam'iyyar adawa a Tanzania za ta yi gangamin farko tun bayan 2016

Bayanai daga Tanzania na cewa dubun dubatar jama’a ne suka hallara a wajen shirye-shirye babban taron motsa jam’iyyar adawa da madugun adawar kasar Freeman Mbowe zai jagoranta. 

Shugaban jam'iyyar adawa ta Chadema Freeman Mbowe a yayin wani gangami.
Shugaban jam'iyyar adawa ta Chadema Freeman Mbowe a yayin wani gangami. Omoo/Open access
Talla

Wannan dai shine karon farko da wata jam’iyyar adawa zata gudanar da gangami tun shekarar 2016 da tsohon shugaban kasar John Magafuli ya haramta tarukan ‘yan adawa a kasar. 

Bayanai sun ce jama’a sun yi ta sowa da ihun ganin jagoran nasu a ganawar farko da suka yi da shi cikin shekaru 7 da suka gabata a babban birnin kasar Dar-es Salam. 

Dage haramcin gudanar da tarukan da fadin albarkacin baki kan ‚yan adawa da shugabanr kasar Samia Suluhu Hassan ta yi ne ya baiwa Freeman Mbowe damar komawa gida da kuma tsayar da ranar gudanar da babban taron motsa jam’iyyar sa ta Chadema. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.