Isa ga babban shafi

Sabon tsarin hadin gwiwa tsakanin Faransa da Burkina Faso

Sakatariyar harakokin wajen Faransa mai kula da huldar kasa da kasa, Chrysoula Zacharopoulou, dake ziyara a birnin Ouagadougou, ta tattauna da shugaban rikon kwarya, Kyaftin Ibrahim Traoré. Tattaunawar ta mayar da hankali kan sabon tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

 Chrysoula Zacharopoulou a birnin Ouagadougou
Chrysoula Zacharopoulou a birnin Ouagadougou AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Tawagar Faransa karkashin jagorancin Sakatariyar harakokin wajen kasar mai kula da bunkasa kasashen renon Faransa da abokan huldar kasa da kasa, Chrysoula Zacharopoulou, ta samu tattaunawa da Shugaba Ibrahim Traoré. tsawon sa'o'i 24.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Faransa da Burkina Faso ta yi tsami, musamman ma da dakatar da RFI, da kuma bukatar korar jakadan Faransa a Burkina Faso, Luc Hallade. Wani batu na rashin jituwa tsakanin Burkina da Faransa:

Bangaren tsaro Sakatariyar harakokin wajen Faransa ta ce Rundunar Sabre, mai sansani a Kamboinsin, wanda ke dauke da sojojin Faransa na musamman na cikin yanayin yaki da ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.