Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci Burkina Faso ta bankado wadanda suka kashe mutane 28

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gudanar da binciken kwakwaf kan musabbabin mutuwar mutane 28 da aka gano gawarsu cikin makon jiya a Burkina Faso.

Kaftin Ibrahim Traoré, shugaban gwamnatin Sojin Burkina Faso.
Kaftin Ibrahim Traoré, shugaban gwamnatin Sojin Burkina Faso. AFP - -
Talla

Hukumar ta bukaci gwamnatin Sojin Burkina Faso ta gudanar da budadden bincike cike da adalci don tabbatar da masu hannu a kisan mutanen 28.

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniyar Volker Turk ya yi maraba da matakin gwamnatin Burkina Fason na shan alwashin gudanar da binciken sai dai ya ce wajibi ne mahukuntan kasar su tabbatar da yin adalci.

A cewar Volker Turk wajibi ne Burkina Faso ta hukunta dukkanin wadanda aka samu da hannu a kisan mutanen 28 ba tare da la’akari da matsayin da suke ko kuma mukamin da suke rike da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.