Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Burkina Faso ba ta da wani dalili na korar Jakadiyarta daga kasar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Burkina Faso ba ta da wani dalili na umurtar babbar Jakadiyarta Barbara Manzi ta fice daga kasar, zalika haramun ne an cirwa jami’ar kariyar diflomasiyyar da dokar kasa da kasa ta ba ta.A  ranar Juma’ar da ta gabata, gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta fitar da wata sanarwa da ke baiwa Manzi, ‘yar kasar kasar Italiya umarnin ficewa daga kasar nan take.

Ibrahima Traoré Shugaban majalisar sojan Burkina Faso
Ibrahima Traoré Shugaban majalisar sojan Burkina Faso © Kilaye Bationo / AP
Talla

Jim kadan bayan sanar da umarnin ne, ministar harkokin waje Olivia Rouamba ta zargi Manzi da yi wa kasar ta Burkina Faso mummunan fata kan yanayin tsaro, wadda tun shekarar 2015 take fama da matsalolin hare-haren ‘yan ta’adda.

Yayin jawabi ta kafar talabijin na kasar, minister harkokin wajen ta ce Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniyar ta yi hasashen aukuwar hargitsi a Burkina Faso, tare da ba da shawarar a kwashe wasu ma'aikatan Majalisar da iyalansu daga Ouagadougou babban birnin kasar.

Ministar  ta ce ko shakkaha babu matakin babbar jami’ar ta kasa da kasa ya karyawa masu zuba hannun jari gwiwa, baya ga haifar da zulumi tsakanin jama’a.

Yanzu haka dai jami’an Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da muhimman ayyuka a Burkina Faso, ciki kuwa har da jigilar rarraba kayayyakin abinci ga dubban kananan yaran da yunwa ta tagayyara a sassan kasar, sakamakon yadda matsalar tsaro ta durkusar da tattalin arzikin kasar da kuma takaita ayyukan sauran kungiyoyin agaji na gida da ketare.

Zuwa yanzu kusan mutane miliyan 2 suka rasa muhallansu, a yankunan arewaci da gabashin Burkina Faso, sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda tun daga shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.