Isa ga babban shafi

Tanzania ta fara bincike kan musabbabin hadarin jirgin da ya kashe mutane 19

Kwararru a Tanzania sun fara bincike don gano musabbabin hadarin jirgin saman kasar a lahadin da ta gabata wanda ya fada cikin ruwa bayan rikitowa lokacin da ya ke tsaka da tafiya a sararin samaniya.

Wani jirgin Tanzania da ya fada cikin ruwa a karshen mako.
Wani jirgin Tanzania da ya fada cikin ruwa a karshen mako. REUTERS - STRINGER
Talla

Mahukuntan Tanzania sun yi umarnin fara binciken ne bayan nasarar tsamo baraguzan jirgin a jiya talata daga tafkin Victoria da ya fada a lokacin faruwar hadarin don kaucewa kamawa da wuta.

Hadarin wanda ya faru a yankin arewa maso yammacin birnin Bukoba irinsa na farko cikin gomman shekaru da ya kashe mutanen da yawansu ya kai 19.

Jirgin wanda ba na ‘yan kasuwa ba ne, da ke dauke da jami’an wani babban kamfani mai zaman kansa a kasar, mutum 43 ke cikinsa lokacin faruwar hadarin ciki har da matukinsa.

Jami’an ‘yan sanda a Tanzania sun dora alhakin faduwar jirgin na karshen mako kan gurbacewar yanayi ko da ya ke sai bayan binciken kwararru ne za a kai ga tabbatar da musabbabinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.