Isa ga babban shafi

Tanzania: Adadin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin sama ya kai 19

Gwamnatin Tanzania ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hadarin da wani karamin jirgin saman fasinja mai dauke da gwamman mutane 43 ya yi a jiya Lahadi ya kai 19.

Masu aikin ceto a Tanzani a yayain da suke kokarin janyo jirgin da ya yi hatsari daga tekun victoria (6 ga Nuwamba, 2022)
Masu aikin ceto a Tanzani a yayain da suke kokarin janyo jirgin da ya yi hatsari daga tekun victoria (6 ga Nuwamba, 2022) REUTERS - STRINGER
Talla

Fariminista Kassim Majaliwa ne ya a bayyana haka a madadin gwamnatin Tanzania, bayan da jirgin saman fasinjan kamfanin Precision Air ya fada kogin Victoria a yayin da yake wucewa ta arewa maso yammacin birnin Bukoba.

Tun da farko mahukuntan yankin sun ce an zaro mutane 26 da suka tsira daga cikin fasinjoji 43 da jirgin ke dauke da su, kuma an garzaya da su asibiti a birnin.

Sai dai a wata sanarwa, kamfanin zirga zirgar jiragen sama ta Precision Air ta ce mutane 24 sun tsira daga wannan hadari, inda wani jami’in kamfanin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa 2 daga cikinsu ma’aikatan aikin ceto ne.

Kamfanin, wanda ya ce ya aike da masu ceto wurin da lamarin ya auku, ya bayyana alhininsa a kan wannan hadari da jirginsa ya yi da misalin karfe 6 saura minti 7 agogon GMT.

Shugaba Samia Suluhu ta aike da sakon ta’aziyya ga wadanda wannan lamari ya shafa, tana mai addu’ar neman taimakon Allah.

Tarayyar Afrika da ofishin jakadancin Amurka a kasar sun aike da sakon jaje, tare da jinjina wa kokarin masu aikin ceto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.