Isa ga babban shafi
Tanzania

Hatsarin mota ya kashe mutum 23 a Tanzania

Akalla mutane 23 ne suka mutu a kasar Tanzania bayan wata mota kirar bas tayi taho mu gama da motar dakon kaya a gabashin kasar ranar Juma'a.

Hadarin mota da ya kashe mutane 30 a Bafia, 30/05/2010.
Hadarin mota da ya kashe mutane 30 a Bafia, 30/05/2010. AFP/STR
Talla

Shugaban ‘yan sanda yankin Morogoro dake gabashin kasar, Fortunatus Muslim, ya ce hatsarin ya afku ne a Melela Kibaoni, mai tazarar kilomita 200 daga birnin gabar tekun kuma cibiyar tattalin arziki Dar es Salaam.

“Direban babbar motar da ke kan hanyarsa daga tashar jiragen ruwa ta Dares Salaam zuwa jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, na kokarin kaucewa wani babur ne a lokacin da motocin biyu suka yi karo da juna.

Fadar shugaban kasar da yammacin ranar Juma'a ta ce mutane 22 ne suka mutu yayin da wasu 38 suka jikkata a hatsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.