Isa ga babban shafi

Kotu ta wanke masu hakar ma'adanan da ake zargi da aikata fyade

Kotu a Afirka ta Kudu, ta wanke wasu masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, su 14 da aka kame bisa tuhumar fyade inda bayan dogon bincike shaidar tantance kwayar halitta ta nuna cewa basu da alaka da laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Wasu da Kotu ke tuhuma a Afrika ta kudu.
Wasu da Kotu ke tuhuma a Afrika ta kudu. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Tun cikin watan Yulin da ya gabata ne, wani gungu masu fyade suka afkawa wani ayarin masu nadar bidiyon waka a gab garin Krugersdorp da ke yammacin birnin Johannesburg tare da yiwa mata 8 fyade mai cike da kankanci, lamarin da ya kai ga kamen akalla masu hakar ma'adanai 80 galibinsu baki da ke aiki ba bisa ka'ida ba a gab da yankin na abin ya faru.

Lamarin wanda ya kai ga tashin hankali baya ga musayar wuta tsakanin 'yan ciranin da jami'an tsaro cikin watan Agusta wanda ya hallaka mutane biyu, gwamnatin Afrika ta kudu ta bayyana shi da mafi munin abin kunya la'akari da cewa dukkanin matan da abin ya shafa kananan yara ne da shekarunsu bai kai 17 ba.

Sai dai bayan dogon bincike kan wannan tuhuma wadda ta ja hankalin duniya musamman kungiyoyin kare hakkin mata, masu hakar ma'adanan 14 da ake zargi da aikata hujjoji sun nuna basu aikata laifin da ake tuhumarsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.