Isa ga babban shafi

Yau za a rantsar da Ibrahim Traore don jagorantar gwamnatin Soji a Burkina Faso

Yau Juma’a za a rantsar da Kaftin Ibrahim Traore a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soji ta rikon kwarya a Burkina Faso, wanda zai mayar da shi shugaban wata kasa mafi karancin shekaru bayan jagorantar juyin mulkin watan jiya.

Sabon shugaban gwamnatin Soji a Burkina Faso Ibrahim Traore.
Sabon shugaban gwamnatin Soji a Burkina Faso Ibrahim Traore. AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Cikin watan Satumban da ya gabata ne Traore, mai shekaru 34, ya jagoranci kananan hafsoshi wajen yin juyin mulki na biyu cikin watanni 8, da ya kawo karshen gwamnatin sojin Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a kasar mai fama da matsalar tsaro da tattalin arziki.

Damiba ya dare mulkin Burkina Faso ne a watan Janairu, bayan hambarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore, sai dai duk da juyin mulkin ba a samu sauyawar matsalolin da kasar ke fuskanta ba, musamman a abin da ya shafi hare-haren ta'addanci da ke ci gaba da salwantar da rayukan daruruwan al'ummar kasa kama daga farar hula da kuma jami'an tsaro.

Dalilin juyin mulkin da kaftin Ibrahim Traore ya yi dai dai da na watan Janairu ne, wato kan gazawar gwamnati wajen kawo karshen hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Burkina Faso da ke sahun kasashe mafiya talauci a Afrika, ta fada halin matsalar tsaro ne tun a shekarar 2014 lokacin da kungiyoyin masu ikirarin jihadi suka fara karfi a makwabtan kasar da suka kunshi Mali da jamhuriyar Nijar, matsalar da zuwa yanzu ta tilastawa 'yan kasar fiye da miliyan 2 barin muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.