Gwamnatin Habasha na fatan warware rikicin arewacin kasar da yan tawaye
Manzon Amurka a yankin Afirka Mike Hammer, ya gana da mataimakin firaministan kasar Habasha Demeke Mekonnen a birnin Addis Ababa a jiya Juma'a, a kokarinsa na kawo karshen rikici a arewacin kasar.
Wallafawa ranar:
Bayan wata ziyara da ya kai a watan Satumba na shekarar nan, Mike Hammer ya koma yankin tun ranar 3 ga watan Oktoba, da fatan ganin an dakatar da tashin hankali a arewacin Habasha nan take da kuma goyon bayan kaddamar da tattaunawar zaman lafiya a karkashin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Amurka.
A farkon watan Oktoba ne gwamnatin tarayya ta Firaminista Abiy Ahmed da wakilan ‘yan tawaye a yankin Tigray suka ce a shirye suke su je tattaunawar da kungiyar kasashen afirka ta AU ta gayyace su a Afirka ta Kudu.
Sai dai ba a iya gudanar da wannan tattaunawa ba, musamman saboda matsalolin kungiyoyi da na kayan aiki, a cewar jami'an diflomasiyya.
A ranar Juma’a, yayin tattaunawa da Hammer, firaministan kasar Habasha Demeke wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, ya jaddada aniyar gwamnati na ganin an warware rikicin arewacin kasar cikin lumana”, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafinta na twitter.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu