Isa ga babban shafi

Mutane 10 sun mutu a wani harin Sojin Saman Habasha kan asibitin

Akalla mutane 10 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a wani luguden wuta ta sama da Sojin Habasha suka yi a yankin Tigray, karo na 2 da irin farmakin ke halaka tarin fararen hula.

Wani hari a birnin Mekele na yankin Tigray a Habasha.
Wani hari a birnin Mekele na yankin Tigray a Habasha. AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

Harin na Sojin Habasha na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan tawayen na Tigray ke mika bukatar tsagaita wuta don kawo karshen yakin wanda ke barkewa a karo na 2 bayan tsagaita wutar tsawon watanni.

Sanarwar da ‘yan tawayen na TPLF ta fitar yau laraba ta ce harin sojin na Habasha kan asibitin da ke Mekele babban birnin yankin ya shafi tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba.

Wani likita a asibitin da aka kaddamar da harin Dr Fasika Amdeslasie ya ce har zuwa yanzu babu cikakkun alkaluman mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata a harin sai dai nan ta ke akwai mutanen biyu da suka mutu.

Luguden wutar Sojin saman na yau, na zuwa bayan harin jirgi marar matuki da aka kai jami’ar Mekele a jiya talata.

Firaminista Abiy Ahmed dai bai ce uffan game da hare-haren na baya-bayan nan ba, dai dai lokacin da kasashen Duniya ke ci gaba da cece-kuce kan hare-haren da ake kaiwa yankin nja Tigray tun bayan dawowar yakin a watan jiya.

Kusan shekaru 2 kenan, ana gwabza yaki tsakanin ‘yan tawayen na yankin Tigray da Sojin gwamnatin Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.