Isa ga babban shafi

An kai harin sama a yankin Tigray na Habasha

An kai wani hari da jirgin sama mara matuki a yankin Tigray na Habasha a wannan Talatar, kwanaki biyu da ‘yan tawayen yankin suka bayyana aniyarsu ta amincewa da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta.

Mayakan TPLF sun zargi sojojin gwamnatin Habasha da kaddamar musu da farmaki gabanin zaman cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.
Mayakan TPLF sun zargi sojojin gwamnatin Habasha da kaddamar musu da farmaki gabanin zaman cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu. © Ben Curtis/AP
Talla

Wani babban jami’in kiwon lafiya da ke aiki a asibitin Ayder Referral Hospital ya ce, harin na sama ya yi sanadiyar raunata akalla mutun guda a babban birnin Mekele da ke yankin na Tigray.

Koda yake kawo yanzu ba a kammala tantance irin girmar barnar da wannan harin ya yi ba, yayin da mayakan TPLF da suka kwashe tsawon shekaru biyu suna fafatwa da sojojin Habasha suka zargi sojojin kasar da kai musu farmakin.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai magana da yawun Kungiyar TPLF, Kindeya Gebrehiwot ya ce, harin na zuwa ne bayan da gwamnatin Tigray ta kafa wata tawagar shiga tsakani tare da bayyana shirinta na tattaunawar zaman lafiya.

Tashar talabijin ta Dimtsi Weyane da ke da alaka da kugiyar TPLF ta yi ikirarin cewa, ita ma an kai mata farmaki, inda har ta gaza ci gaba da watsa shirye-shiryenta, sakamakon lalata mata kayayyakin aiki.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya gaza tantance gaskiyar ikirarin gidan talabijin din saboda wahalar kutsawa cikin yankin arewacin Habasha, sannan kuma ga matsalar katsewar hanyoyin sadarwa.

Har yanzu Firaministan Habasha Abiy Ahmed bai ce uffam ba a game da wannan harin na jirgin sama mara matuki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.