Isa ga babban shafi

Jakadan Amurka na musamman ya isa Habasha don sasanta rikicin Tigray

Jakadan Amurka na musamman Mike Hammer ya isa Habasha don tattaunawa da gwamnatin kasar a wani yunkuri na ganin an sulhunta bangarorin da ke yakar juna da nufin tsagaita wuta a sabon yakin da ya sake barkewa a karshen watan jiya.

Jakadan Amurka na musamman Habasha Mike Hammer.
Jakadan Amurka na musamman Habasha Mike Hammer. AFP - ORLANDO SIERRA
Talla

A karshen watan jiya ne yaki ya dawo sabo tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen na Tigray a yankin arewacin kasar bayan da bangarorin biyu suka zargi juna da karya ka’idojin da ke kunshe a kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar da suka kulla.

Tun a karshen mako ne Amurka ta sanar da Hammer a matsayin jakadan wanda ta nemi ya yi aiki tukuru don farfado da fatan yiwuwar kulla yarjejeniyar zaman lafiya da za ta kawo rikicin bangarorin biyu.

Tuni dai aka yi wata ganawa ta musamman tsakanin Hammer da jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman Hanna Serwaa Tetteh da ke jagorancin shirin kawo karshen rikicin na Habasha.

Ko a ziyarar da ya kai watan jiya tare da Jakadan Tarayyar Turai Annette Weber, Hammer ya kai ziyarar gani da ido yankin na Tigray da yaki ya daidaita inda suka roki bangarorin biyu da su tabbatar da kawo karshen rikicin.

Bayanai dai sun ce Hammer zai yi ganawa ta musamman da Firaminista Abiy Ahmed, sai dai har zuwa yanzu babu bayani kan yadda ganawar za ta guda walau daga gwamnatin Habasha ko kuma Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.