Isa ga babban shafi

Hukumar kare hakkin dan ta MDD ta tsawaita aikinta a Habasha

Hukumar kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar kara wa'adin shekara guda na aikin kwamitin kwararru da ke da alhakin gudanar da bincike kan kare hakkin bil'adama a kasar Habasha mai fama da rikici.

Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya.
Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya. AFP - ANDREA RENAULT
Talla

Kasashe 21 ne suka amince da kudurin da Tarayyar Turai ta gabatar, yayin da wasu kasashen 19 suka hau kujerar naki, cikinsu kuwa har da daukacin mambobin hukumar kare hakkin bil'adama na Afirka in ban da Malawi da ta ki kada kuri'a tare da wasu kasashe guda shida.

Wani lokaci nan gaba, kwararrun za su gabatar da rahoton baka kan halin da ake ciki a kasar Habasha da ke fama da tashe tashen hankula, musamman a yankin Tigray, tun watan Nuwamban shekarar 2020.

Za a gabatar da rahoton ne kuma yayin zama na gaba da hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya za ta yi a farkon shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.