Isa ga babban shafi

Kanal Assimi Goita ya karbi daftarin sabon kundin tsarin mulkin Mali

Shugaban mulkin sojan Mali Kanal Assimi Goita ya karbi daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar a jiya talata, matakin da ke zama muhimmin bangare na yunkurin da sojoji ke yi, a kokarin ci gaba da rike madafun ikon kasar mai fama da hare-haren ta'addanci har zuwa shekara ta 2024.

Shugaban kasar Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban kasar Mali Kanal Assimi Goita. AP
Talla

Har yanzu dai ba a bayyana abubuwan da ke kunshe cikin daftarin sabon kundin tsarin mulkin ba, wanda aka mikawa shugaban kasar ta Mali watanni biyu, bayan lokacin da aka tsara za a kammala rubuta shi.

Mahukunta Mali, wadanda sojojin da suka kwace mulki a watan Agustan shekarar 2020 suka mamaye, sun bayyana rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar a matsayin daya daga cikin muhimman sauye-sauyen da ake bukata a kasar ta Mali.

Fiye da shekaru 10 kenan Mali na fama da hare-haren ta'addancin kungiyoyi masu ikirarin jihadi wanda ya haddasa juyin mulki har sau 2 cikin shekara guda a kasar duk dai a yunkurin kawo karshen matsalar da ta haddasa asarar rayukan dubunnan 'yan kasar da suka kunshi jami'an tsaro da fararen hula.

Ana saran sabon kundin tsarin mulki ya tafi kafada-da-kafa da bukatar Sojojin da ke mulkin kasar wadanda suka samar da muhimman sauye-sauye ciki har da katse huldar tsaro da Faransa uwar goyonsu da kuma bukatar ficewar duk wasu sojojin ketare daga kasar.

Tun bayan hawan Goita mulkin Mali ne, shugaban ya kulla kwantiragin da ya kawo sojojin hayar kamfanin Wagner mallakin Rasha cikin kasar da nufin taimakawa a yaki da ta'addanci, sai dai bayanai na nuni da cewa Sojin hayar na fuskantar tirjiya a yakin da suke cikin kasar ta yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.