Isa ga babban shafi

Sojojin Mali sun halaka 'yan ta'adda 41

Rundunar sojin kasar Mali ta sanar da halaka 'yan ta'adda 41 a yankin tsakiyar kasar, inda ‘yan kwanakin da suka gabata maharan suka kashe fararen hula 53.

Sojojin gwamnatin Mali a garin à Goundam, kusa da Tombouctou.
Sojojin gwamnatin Mali a garin à Goundam, kusa da Tombouctou. AFP/PHILIPPE DESMAZES
Talla

An dai samub wannan nasara ce daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban da muke, 'inda dakaru tare da samun goyon bayan hare-hare ta sama, suka kai samame a yankin Tiemaba da Bamada, domin farautar wata kungiyar ta'addanci da ta yi kaurin suna wajen cin zarafin fararen hula.

Sanarwar ta kara da cewar, baya ga gwamman ‘yan ta’adan da suka halaka, sun kame wasu akalla 33, cikinsu kuwa har da wasu kasurguman mugaye 15 da aka dade ana nema ruwa a jallo.

Mali dai ta fada cikin rashin tsaro tun a shekarar 2012, saboda hare-haren ta'addanci da rikice-rikicen kabilanci, lamarin da ya tilastawa iyalai da dama yin kaura daga yankunansu, wasunsu ma suka fice daga kasar, duk da tura dakarun Majalisar Dinkin Duniya na rundunar MINUSMA da kuma dakarun G5 Sahel na yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.