Isa ga babban shafi

Mali za ta fara shigar da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro aikin Soja

Gwamnatin Mali ta amince da wani sabon kudirin doka da ya tanadi shigar da 'yan sanda da sauran jami’an tsaro cikin aikin Soja.

Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita. AP - Baba Ahmed
Talla

Da wannan mataki, gwamnati za ta samu damar jibge ‘yan sandan a yankunan da sojoji suka kwato daga hannun ‘yan ta’adda domin tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu da kuma hana dawowar kungiyoyi masu dauke da makamai.

Haka kuma tanadin dokar zai tilastawa jami’an kwana-kwana marawa sojojin da ke yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a bakin daga baya.

Ko da ya ke har yanzu wannan kudiri na bukatar amincewar majalisar rikon kwarya ta kasar, wacce ta kasance majalisar dokoki tun bayan da sojoji suka karbe mulki da karfin tuwo a shekarar 2020 kafin ya zama doka.

Matakin na daga cikin shawarwarin da aka amince da su yayin babban taron kasar da majalisar mulkin soji ta shirya a watan Disamban bara, a matsayin mafita daga rikicin kasar da yaki ci yaki cinyewa.

Da wannan mataki ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron farin kaya za su ci moriyar albashi da sauran alawus dai-dai da sojoji.

Sai dai wannan sabon matsayi zai kuma hana su 'yancin shiga yajin aiki ko shiga wata kungiyar kwadago ko kuma gudanar da zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.