Isa ga babban shafi

Habasha: Gwamnati da 'yan tawayen Tigray sun amince da fara tattaunawa

Gwamnatin Habasha da 'yan tawayen yankin Tigray sun ce shirye su ke su halarci tattaunawar sulhu da kungiyar kasashen Afirka ta gayyace su wadda za ta gudana a Afirka ta Kudu cikin watan nan da nufin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed AP - Mulugeta Ayene
Talla

Mai bai wa Firaminista Abiy Ahmed shawara kan harkokin tsaro ya ce gwamnati ta karbi goron gayyatar, yayin da jagoran ‘yan tawayen Tigray shi ma ya ce a shirye suke su aika da wakilansu zuwa tattaunawar sulhun.

Sai dai bangaren 'yan tawayen na Tigray sun diga ayar tambaya kan tsarin da za a bi wajen ganawar, dai dai lokacin da bangarorin biyu ke ci gaba da farmakar juna.

Fada ya sake barkewa tsakanin sojojin Habasha da ‘yan tawaye Tigray a karshen watan Agusta, lamarin da ya kawo karshen tsagaita wuta na tsawon watanni biyar tare da dakatar da kai agaji zuwa yankin Tigray, inda karancin abinci, da magunguna ya tagayyara miliyoyin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.