Isa ga babban shafi

Liberia ta kwace hodar iblis da darajarta ta kai dala miliyan 100

Hukumomin kasar Liberia sun sanar da kwace hodar ibilis da aka bayyana kudin ta akan Dala miliyan 100, sakamakon wani hadin kan da suka yi da abokan aikin su na kasar Amurka.

Hodar Iblis.
Hodar Iblis. © photopixel/ Shutterstock
Talla

Ministan shari’ar kasar Musa Dean ya shaidawa manema labarai cewar, Hukumar yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ce da taimakon takwarorinta na Amurka suka kwato wannan hodar a kauyen Topoe dake Yammacin Birnin Monrovia.

Dean yace sun kama wani dan kasar Guinea Bissau da wani dan kasar Lebanon wadanda ake zargin suna da hannu wajen safarar hodar.

Shugaban Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyin Marcus Zehyoue yace tuni suka kaddamar da gagarumin bincike domin gano duk wadanda suke da hannu a cikin safarar hodar.

Ofishin Jakadancin Amurka a Liberiya ya jinjinawa hukumomin Liberia saboda rawar da suka taka wajen kama hodar mai dimbin yawa.

Sanarwar tace wannan gagarumar nasara ta tabbatar da hadin kan dake gudana tsakanin Liberia da Amurka da kuma Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.