Isa ga babban shafi

Afrika ta kudu za ta samar da karin cibiyoyin lantarki na zamani 25

Afirka ta Kudu ta rattaba hannu akan yarjejeniyar samar da hasken wutar lantarki na zamani, wanda baya gurbata muhalli, kwanaki bayan da kasar ta tsunduma cikin duhu, sakamakon tabarbatrewar harkar samar da wutar.

Wasu cibiyoyin lantarki na zamani a Afrika ta kudu.
Wasu cibiyoyin lantarki na zamani a Afrika ta kudu. Wikimedia
Talla

Gwamnatin Afrika ta kudu ta gabatar da shirin samar da tashoshin samar da wutar ta hanyar iska da kuma hasken rana 25, wadanda ake saran su samar da megawatts dubu 2 da 583, wanda zai zama karin kashi 4 da rabi na wutar da kasar ke samu yanzu haka.

Kamfanin Eskom da ke amfani da makamashin kwal wajen samar da wutar, na samar da megawatts dubu 26 kowacce rana, sabanin megawatts dubu 32 da ake bukata.

Karancin lantarki ya zama babbar matsala ga al'ummar Afrika ta kudu kasar da ke fuskantar matsananciyar tsadar rayuwa sakamakon tashin farashin man fetur lamarin da ya tilasta shugaba Cyril Ramaphosa kiran taron gaggawa don tattaunawa kan batun.

Ko a watan jiya anga yadda dubunnan al'ummar kasar suka bazu kan titunan birnin Pretoria don gudanar da zanga-zangar bukatar neman sauki kan halin da suke ciki na tsadar kayaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.