Isa ga babban shafi

Saudiya ta kaiwa Somalia agajin ton 70 na abinci don magance yunwa

Kungiyar agaji ta Sarki Salman a Saudi Arabia ta aike da agajin kayakin abincin da yawansu ya kai tan 70 zuwa ga yankin Gersbali na Somalia sakamakon tsanantar yunwa da ke da nasaba da karancin ruwan saman da ya hana harkokin noma tare da haddasa fari.

Somaliya na sahun kasashen Afrika da yanzu haka suke fama da matsananciyar yunwa sakamakon fari.
Somaliya na sahun kasashen Afrika da yanzu haka suke fama da matsananciyar yunwa sakamakon fari. AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Somalia na daga cikin kasashen Afrika da yanzu haka ke fuskantar matsananciyar yunwa sakamakon fari biyo bayan karancin zubar ruwan sama tsawon shekarun 6 a jere.

A jiya alhamis ne kayakin abincin suka isa yankin na Gersbali inda ake da kaso mai yawa na ‘yan gudun hijirar da suka yi kaura daga yankunansu saboda matsananciyar yunwa.

Kamfanin dillancin labaran Saudi Arabia ya bayyana cewa Iyalai dubu 6 ne yanzu haka suka amfana da agajin abincin.

Agajin abincin wani bangare ne na kokarin masarautar Saudi Arabia don samar sauki ga wadanda matsalar fari ta shafa a kasar ta Somalia.

Wasu bayanai sun ce Kungiyar agajin ta sarki Salman ta gudanar da aikin ginin rijiyoyin burtsatse da matsugunan wucin gadi baya ga kayakin agaji na lafiya ga dubunnan mutanen da fari ya koro daga yankunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.