Isa ga babban shafi

'Yan Somalia sun fara mutuwa saboda yunwa - WHO

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai alamun da ke nuna cewar wasu daga cikin mutanen kasar Somalia da ke fama da matsalar fari sun fara mutuwa, inda ta yi gargadin cewar ma’aikatan agaji ba za su iya samar wa jama’a abincin da suke bukata ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ana bukatar karin miliyoyin Dala domin ceto mutanen da ke cikin bala'in fari a Somalia
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ana bukatar karin miliyoyin Dala domin ceto mutanen da ke cikin bala'in fari a Somalia REUTERS/Ismail Taxta
Talla

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya ce yanayin halin da ake ciki abin tada hankali ne, saboda yadda aka bayyana cewar wani sashe na yankin kasar na fuskantar bala’in yunwar da za ta hallaka jama’a muddin ba a dauki matakin kai musu dauki ba.

Gebreyesus ya shaida wa manema labarai a Geneva cewar, miliyoyin jama’ar kasar ne ke fuskantar wannan matsala ta yunwa, kuma yanzu haka akwai alamun da ke nuna cewar yunwar ta kashe wasu daga cikinsu.

Shugaban Hukumar ya ce duk da yake an dan samu ci gaba wajen tallafin da kungiyoyin agaji ke kai wa Somalia, ya zama wajibi hukumarsa da wasu kungiyoyi su taimaka wajen dakile wannan matsala duk da karancin kudaden da suke fuskanta.

A jiya Talata, mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da aikin jinkai, Martin Griffiths ya ce ana bukatar karin Dala biliyan guda akan Dala biliyan guda da miliyan 400 da aka ware domin ceto mutanen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.