Isa ga babban shafi

Kusan rabin al'ummar Somalia na fama da yunwa - Rahoto

Kungiyar agaji ta ‘Save the Children’ ta yi gargadin cewa kasashen duniya na yin sakaci wajen daukar matakan dakile bala'in yunwa a Somalia, a yayin da kuma yara ke mutuwa saboda gazawar ayyukan asibitoci saboda yawan da aka yi musu.

Wasu 'yan kasar Somalia dake gudun hijira a garin Shebelle, mai nisan kilo mita 50 daga birnin Mogadishu.
Wasu 'yan kasar Somalia dake gudun hijira a garin Shebelle, mai nisan kilo mita 50 daga birnin Mogadishu. Reuters/Feisal Omar
Talla

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a wannan watan, ya ce kimanin 'yan Somalia miliyan 7 da dubu 100, kusan rabin al'ummar kasar, na fama da yunwa, yayin da sama da 200,000 ke gab da fadawa cikin yunwar.

Somalia da makwabtanta dake yankin kuryar gabashin Afirka da suka hada da Habasha da Kenya na fuskantar Fari mafi muni a cikin shekaru sama da 40, biyo bayan rashin saukar damina tsawon shekaru 4, lamarin da ya lalata amfanin gona da kuma haddasa mutuwar dabbobi.

Yanzu haka dai kungiyoyin bayar da agaji sun ce akwai karancin kudaden tallafi daga kasashen duniya ga Somalia, inda ya zuwa yanzu kiraye-kirayen bayar da gudunmuwar ya tara kasa da kashi 30 cikin 100 na dalar Amurka biliyan 1 da kusan rabi da ake bukata domin magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.