Isa ga babban shafi
Afirka - karancin abinci

Kasashen gabashin Afirka na fuskantar barazanar yunwa - Oxfam

Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa mutane kusan miliyan 28 a gabashin Afirka na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa saboda tashin farashin kayayyaki da ya samo asali daga rikicin Rasha da Ukraine da kuma jinkirin saukar damunan bana .

Akasari yankunan da ke fama da rikici ne ke fuskantar matsalar yunwa.
Akasari yankunan da ke fama da rikici ne ke fuskantar matsalar yunwa. Oxfam East Africa
Talla

Kungiyar agajin ta ce kasashen Kenya da Somaliya da Habasha sun fuskanci fari mafi muni cikin shekaru 40, yayin da Sudan ta Kudu ke fama da matsalar ambaliyar ruwa.

Yakin Rasha da Ukraine

Har ila yau, kungiyar ta bayyana damuwa dangane da yadda hankalin kasashen duniya ya karkata kan yakin Rasha da Ukraine, lamarin da ya kai ga watsi kan matsalar karancin abinci da ake fuskanta masamman a gabashin Afirka.

Cikin sanarwa da ta fitar, Oxfam ta ce gidauniyar Majalisar Dinkin Duniya ta 2022 ta tarawa kasashen Habasha da Somaliya da Sudan ta Kudu kudaden agaji na tafiyar hawainiya, inda ya zuwa yanzu kashi 3 cikin ɗari kachal aka samu na dala biliyan 6 da ya kamata a samar.

Babban bala'i

A cewar darektan zartarwa na kungiyar Oxfam Gabriela Bucher, "Yankunan Habasha, Kenya, Somaliya, Sudan ta Kudu da sauran su na fuskantar babban bala'I, duk da cewa yankin na dakon ruwan sama cikin wannan watan, zai yi wuya sus amu cikakken murmurewa, muddun ba a dauki matakin gaggawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.