Isa ga babban shafi

Somalia na kan iyakar tsunduma cikin yunwa - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, Somalia wadda ke fama da matsalar fari, na gab da tsunduma cikin ibtila’in yunwa a karo na biyu cikin shekaru 10, yayin da Majalisar ta ce, lokaci na kurewa na ceto ‘yan kasar daga musibar.

Dabbobi sun mutu sakamakon rashin ruwan sama a Somalia
Dabbobi sun mutu sakamakon rashin ruwan sama a Somalia AP - Mulugeta Ayene
Talla

Shugaban Kula da Ayyukan Jin-Kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya shaida wa manema labarai a birnin Mogadishu cewa, yunwa na nan a kan bakin kofar Somalia, yana mai cewa, sun samu gargadi na karshe.

Wani rahoto kan abinci da aka fitar a wannan Litinin na nuni da cewa, matsalar ta yunwar za ta karade yankunan Baidoa da Burhakaba da ke kudu maso tsakiyar kasar ta Somalia tsakanin watan Octoba zuwa Disamba.

Babban Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, ya kadu matuka a ‘yan kwanakin nan kan yadda suka ga mutanen Somalia ke cikin radadi da wahala.

A cewarsa, rashin wadataccen ruwan sama da gomman shekaru na rikici da raba jama’a da muhallansu da tabarbarewar tattalin arziki, sune suka jefa dimbin ‘yan Somalia cikin barazanar yunwa.

Somalia da makwabtanta Habasha da Kenya dukkaninsu na gab da fuskantar fari mafi muni cikin shekaru 40 a yankin gabashin Afrika sakamakon rashin ruwan saman a tsawon kaka hudu, lamarin da ya yi sanadin ajalin dabbobi da rashin albarkatun gona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.