Isa ga babban shafi

Afrika ta bukaci manyan kasashe su cika alkwarinsu na zuba kudi don yakar dumamar yanayi

Shugabannin kasashen Afrika fiye da 24 sun bukaci mawadatan kasashe su tabbatar da aniyar da suka dauka ta zuba makudan kudade a yaki da dumamar yanayi don taimakawa nahiyar ta magance illar da tuni sauyin yanayin ya fara haifar mata.

Wani taron shugabannin kasashen Afrika kan yanayi.
Wani taron shugabannin kasashen Afrika kan yanayi. REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Kasashen na Afrika wadanda ke dora alhakin gurbata yanayi kan manyan kasashe, kiran na su na zuwa ne bayan kakkausar suka game da yadda manyan kasashen da ke da kamfanoni masu gurbata muhalli suka kauracewa taron nahiyar na Netherland da ke shirin tallafawa Afrika da kudaden yaki da matsalar ta dumamar yanayi.

Wata sanarwar hadaka da kasashen 24 suka fitar bayan kammala taronsu a birnin Cairo na Masar gabanin fara babban taron majalisar dinkin duniya na COP27 da kasar za ta karbi bakonci, sun bukaci kasashen su sauke nauyin da ke kansu wajen cika alkawuran da suka dauka kan yaki da dumamar yanayi.

Taron kasashen da ya samu halartar shugabanni 24 na nahiyar na zuwa ne watanni biyu gabanin babban taron na COP27 da majalisar dinkin Duniya za ta jagoranta a Masar wato cikin watan Nuwamba.

Ko a farkon makon nan, tsohon magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana cewa kasashen Afrika na samar da akalla kashi 3 ne kadai na tiririn da ke gurbata muhalli.

Sai dai duk da haka nahiyar ta Afrika ita ce mafi wahaltuwa daga illar da dumamar yanayi ta fara yiwa duniya, inda aka fara fuskantar tsananin fari a wasu yankuna saboda karancin zubar ruwan damuna yayinda a wasu yankuna ake ganin zubar ruwan ba kakkautawa wanda ya haddasa ambaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.