Isa ga babban shafi

Kerry zai gana da shugabannin Afirka a Masar kan sauyin yanayi

Sakataren harkokin muhallin Amurka, John Kerry ya bayyana fatar ganin taron sauyin yanayin da aka yiwa lakabi da COP27 da zai gudana a kasar Masar, ya samar da yanayin da zai sauya duniya.

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry kenan, wanda yanzu ke a matsayin sakataren harkokin muhallin kasar
Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry kenan, wanda yanzu ke a matsayin sakataren harkokin muhallin kasar © REUTERS
Talla

Kerry wanda ya isa Alkahira tare da shugabannin kasashe 24 na Afirka domin halartar taron share fage na kwanaki 3 da zai shata yadda taron COP27 zai gudana a Sharm el Sheikh, na zuwa ne kwana biyu bayan kammala taron Rotherdam, inda shugabannin Afirka suka cacaki takwarorin su na kasashen da suka ci gaba, saboda kauracewa taron da kuma kin cika alkawarin bada kudaden da suka yi alkawari, domin rage radadin da kasashe masu tasowa ke fuskanta sakamakon illar sauyin yanayi.

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya jaddada cewar, nahiyar Afirka na fitar da kashi 3 ne kacal na sinadarin dake gurbata muhalli, amma kuma suna daga cikin yankunan da suka fi shan radadin matsalar da ake samu.

John Kerry yace taron da za’ayi a watan Nuwamba zai bada damar sauya duniya, ganin irin matsalolin da suka addabi duniyar a yau.

Shugaban kasar Masar Abdel Fatah al Sisi yace ana bukatar Dala biliyan 800 kowacce shekara domin rage radadin da matsalar sauyin yanayi ke haifarwa.

Bayan shugabannin Afirka dake halartar taron, akwai Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed da kungiyoyin kare muhalli da kamfanoni masu zaman kansu da kuma masana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.