Isa ga babban shafi

Mali ta roki mayar da ita cikin AU tare da janye mata takunkumai

Mali ta roki kungiyar tarayyar Afrika ta janye takunkuman da ta lafta mata bayan kasar ta fuskanci juyin mulki har sau 2 cikin kasa da shekara guda baya ga gazawarta wajen komawa karkashin mulkin farar hula.

Sau 2 Mali na fuskantar juyin mulkin Soji cikin kasa da shekara guda.
Sau 2 Mali na fuskantar juyin mulkin Soji cikin kasa da shekara guda. © Misper Apawu / AP
Talla

A watan Agustan 2020 ne Mali ta gamu da juyin mulkin farko gabanin sake fuskantar wani juyin mulkin a watan Mayun 2021, wanda ya sanya kungiyar ta AU lafta mata takunkuman karya tattakin arziki.

A watanni 2 da suka gabata ne Mali ta samu sassaucin wasu takunkumai da ke kanta bayan da ta bayar da tabbaci da kuma lokacin gudanar da zaben shugaban kasa don komawa karkashin mulkin farar hula.

A jawabin ministan wajen Mali Abdoulaye Diop gaban taron AU a Togo ya ce babban abin da ke gaban gwamnatin Sojin a yanzu bai wuce ganin ta jagoranci gudanar da sahihin zaben da zai mayar da kasar turbar demokradiyya ba a cikin watanni 24 daga watan Maris din shekarar nan.

A cewar Diop ko kadan gwamnatin Sojin ba ta da shirin juya baya kan alkawarin da ta dauka, wanda kuma wani dalili da jajircewar da Malin ke nunawa ne ya dace a bata damar komawa cikin AU da kuma janye mata takunkuman da ke kanta.

Tun bayan juyin mulkin 2021 ne dai kasar ta yankin Sahel mai fama da tashe-tashen hankula da kuma hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi, ta fice daga kungiyoyin AU da ECOWAS sakamakon yadda ta ki amincewa da sharuddan da suka gindaya mata na mika mulki ga farar hula nan ta ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.