Isa ga babban shafi

Bangarorin da ke rikici a Habasha sun kai wa juna munanan hare-hare

Rahotanni daga Habasha na cewa bangarorin da ke yakar juna a kasar sun ci gaba da kai farmaki ba kakkautawa bayan dawowar yakin a farkon makon nan.

Wani yanki na Merkele da Sojin Habasha suka kai wa hari.
Wani yanki na Merkele da Sojin Habasha suka kai wa hari. AP
Talla

Bayan ‘yan tawayen na Tigray sun zargi Sojin Habasha da hadin gwiwar Sojin Eritrea da kai musu wasu muggan hare-hare a jiya alhamis, wasu majiyoyi sun ce ‘yan tawayen sun mayar da martani.

Akwai dai fargabar yakin ya sake munana a wannan karon la’akari da yadda kowanne bangare ya yi watsi da kwarya-kwaryar yarjejeniyar da aka cimma watanni 21 a baya wadda aka yi fatan ta kai ga kulla yarjejeniyar zaman lafiyar da za ta kawo karshen yakin na kusan shekaru 2.

Duk rahotanni da ke cewa dakarun Sojin Habasha sun fara wani kakkrfan atisaye a arewacin yankin na Tigray da ke gab da Eritrea, har zuwa yanzu gwamnatin Abiy Ahmed ba ta ce uffan kan zarge-zargen ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.