Isa ga babban shafi

Habasha: An yi ta gwabza fada a yankin Amhara duk da yarjejeniyar zaman lafiya

An sake gwabza fada a arewacin kasar Habasha, kusa da kudu maso gabashin yankin Tigray, tsakanin dakarun 'yan tawaye da sojojin gwamnati, wadanda ke cikin rikici tun watan Nuwamban 2020, abin da ya kawo karshen zaman sulhu na tsawon watanni biyar.

Rahotanni sun yi kiyasin cewa mutane sama da dubu guda da suka tsere daga fadan sun fake a Woldiya, wani gari mai kusan mutane 100,000.
Rahotanni sun yi kiyasin cewa mutane sama da dubu guda da suka tsere daga fadan sun fake a Woldiya, wani gari mai kusan mutane 100,000. AP - Ben Curtis
Talla

"An yi kazamin fada a nan kusa da mu. Na ji karar manyan makamai tun da safe" har zuwa la'asar, a cewar wani mazaunin Kobo da ke shaidawa AFP.

“Yanzu haka mutane da yawa da suka rasa matsugunansu na tahowa daga yankunan Gobye da Robit”, tsakanin Kobo da Woldiya, kuma “yanayin Woldiya na cike da rashin tabbas,” in ji   Wulda wani dan gudun hijira.

Firayim Minista Abiy Ahmed, y ace sojojin sun janye daga Kobo, dake da tazarar kilomita 15 kudu da kan iyakar Tigray, domin kauce wa hasarar rayuka da dama, yayin da ‘yan tawayen Tigrai suka kai wa birnin hari daga wurare da dama.

Wata majiyar diflomasiyya ta bayar da rahoton cewa, an gwabza fada a wani wuri makamancin haka tsakanin garuruwan biyu, yayin da wata majiyar jin kai ta bayyana cewa, ana gwabza kazamin fada a tsaunin Zobel da ke kudu maso gabashin Kobo.

Hukumomi a garin Woldiya sun sanya dokar hana fita daga karfe 19:00 zuwa 06:00 na safe da kuma zirga-zirgar motoci daga karfe 18:00 na safe.

Wakilin AFP ya gano yadda motocin daukar marasa lafiya dauke da sojoji da suka jikkata da kuma sojojin yankin Amhara da kuma mayakan fano na Amhara, wadanda dukkansu ke goyon bayan sojojin gwamnatin kasar.

Rahotanni sun yi kiyasin cewa mutane sama da dubu guda da suka tsere daga fadan sun fake a Woldiya, wani gari mai kusan mutane 100,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.